Babban lauya kuma SAN, Femi Falana, ya bukaci a haramta amfani da kafafen sada zumunta ga yara ’yan kasa da shekara 16 a Nijeriya, yana mai cewa hakan na da muhimmanci domin kare lafiyar tunani da tarbiyyar yara.
Falana ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Lagos, yayin bikin kaddamar da gasar Dare2Debate, inda ya ce kasashe da dama a duniya sun fara daukar irin wannan mataki, yana mai ambaton Ostiraliya da ta haramta wa yara ’yan kasa da shekara 16 shiga kafafen sada zumunta.
Ya kara da cewa dole ne Nijeriya ta bi wannan hanya domin amfanin yara, yana mai cewa dole a tsara ka’idoji da dokoki da za su daidaita amfani da kafafen zamani, saboda tasirin da suke da shi kan rayuwar matasa da makomar al’umma.



