Shugaban matatar man Dangote, Aliko Dangote, ya ce kungiyoyin da ke zagon kasa a bangaren mai da gas a Najeriya da ya kira “oil mafia” sun fi karfin masu safarar kwayoyi.
Ya bayyana cewa an saci kayan matatar Dangote da darajarsu ta kai $82m, lamarin da ya janyo karin tsaro a matatar.
Dangote ya ce an yi gagarumin zagon kasa, har da cire muhimmin sashi daga babbar injin tukunyar ruwa yayin aiki, da kuma lalata bututun man fetur a fadin kasa. Ya ce wadannan ayyuka na nufin kassara aikin tace mai a cikin gida domin ci gaba da dogaro da shigo da fetur.
Jaridar Punch ta ruwaito shi na jaddada cewa zagon kasar da ake yi wa matatun mai na cikin gida na barazana ga tattalin arzikin kasa.



