Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa dole na iya sanyawa jam’iyyar ta shiga kawance da wasu jam’iyyu idan ƙoƙarin da ake yi na warware rikicin cikin gida bai yi nasara ba.
Alhaji Sule Lamido ya yi wannan furucin ne yayin da yake karɓar shugabanni da masu ruwa da tsaki na PDP daga Jihar Jigawa a ofishinsa da ke Kano, inda ya jaddada buƙatar gaggauta sulhu domin ceto jam’iyyar daga ci gaba da durƙushewa.
Ya bayyana cewa rashin haɗin kai da sulhu na iya ƙara raunana PDP, yana mai kira ga shugabanni da mambobin jam’iyyar da su fifita haɗin kai da sasanci don dawo da ƙarfinta a siyasar Nijeriya.



