Jam’iyyar APC ta yi nasara a dukkan kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 27 da kuma na kansiloli a zaben ƙananan hukumomi da aka gudanar a Jihar Borno ranar 13 ga Disamba.
Shugaban Hukumar Zaben Jihar Borno (BOSIEC), Alhaji Tahiru Shettima, ne ya sanar da sakamakon a Maiduguri, yana mai ayyana zaben a matsayin sahihi, mai cike da adalci kuma a bayyane.
Shettima ya ce jam’iyyu shida ne suka shiga zaben duk da cewa BOSIEC ta bai wa kowa dama kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



