DCL Hausa Radio
Kaitsaye

FIFA ta sanya $60 a matsayin kudin tikitin kallon kofin duniya na 2026

-

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ƙaddamar da sabon rukuni na tikiti a dalar Amurka 60 ga kowane ɗayan wasannin 104 na Gasar Kofin Duniya ta 2026 a Amurka, Kanada da Mexico, bayan korafin magoya baya kan tsadar tikiti.
FIFA ta ce tikitin na $60 za a keɓe shi ne ga masu goyon bayan ƙungiyoyi da suka cancanta, kuma zai zama kashi 10 cikin ɗari na rabon kowace ƙungiyar ƙasa.
An bayyana cewa tsarin an tsara shi ne domin taimaka wa magoya baya masu biye da ƙungiyoyinsu a gasar.
Sai dai ƙungiyar magoya baya ta Football Supporters Europe (FSE) ta ce tikitin bai isa ba, tana mai cewa mafi yawancin magoya baya har yanzu za su ci gaba da biyan tsadar tikiti fiye da kowace gasar da ta gabata.
Haka kuma an yi suka kan rashin samar da tikitai na musamman ga masu nakasa da abokan tafiyarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a Ingila

Ƙungiyar British Medical Association (BMA) ta tabbatar da ci gaba da gudanar da yajin aiki, bayan kashi 83 cikin ɗari na mambobinta sun amince da...

Tsohon Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya yi ritaya

Tauraron ƙwallon ƙafa Ahmed Musa ya sanar da yin murabus daga buga wa Najeriya ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa, bayan shekara 15 yana taka leda...

Mafi Shahara