Babbar Kotun Jihar Kano da ke zama a Kano Municipal ta yankewa wata mace mai suna Hafsa Umar hukuncin daurin shekara 10 a gidan gyaran hali bayan ta same ta da laifin ajalin ’yar mijinta.
Kotun ta saurari cewa Hafsa ta yi wa yarinyar duka ne bayan zargin ta da satar kuli-kuli, inda masu gabatar da ƙara suka bayyana cewa dukan ya wuce kima har ya jawo mutuwar yarinyar.
Rahoton jaridar Daily Trust ya ce a yayin shari’ar, lauyar gwamnati Barrista Hafsa Adam da Barrista Jamilu Abubakar sun gabatar da shaidu da hujjoji domin tabbatar da laifin wadda ake tuhuma, yayin da bangaren kariya ya gabatar da shaidu biyu.
Da take yanke hukunci, Mai shari’a Aisha Mahmud ta ce ɓangaren ƙara ya tabbatar da laifin wanda ake tuhuma ba tare da shakka ba.
Alkalin kotun ta bayyana cewa laifin ya saba wa Sashe na 226 na Kundin Hukunta Laifuka (Penal Code), tare da yanke mata hukuncin shekara 10 a gidan gyaran hali.



