Ƙungiyar British Medical Association (BMA) ta tabbatar da ci gaba da gudanar da yajin aiki, bayan kashi 83 cikin ɗari na mambobinta sun amince da a kuri’ar intanet, duk da sabon tayin da gwamnati ta gabatar.
Yajin aikin likitocin da aka fi sani da resident doctors (masu neman kwarewa) zai fara ne da karfe 7:00 na safiyar Laraba.
Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, ya bayyana takaicinsa, yana mai kiran matakin da “rashin ɗa’a”, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar matsin lamba daga cutar mura (flu) a kasar.
Gwamnati ta ce sabon tayin bai shafi karin albashi ba, tana mai cewa albashin likitocin ya riga ya ƙaru da kusan kashi 30 cikin ɗari cikin shekaru uku, yayin da BMA ke jaddada cewa albashin su ya ragu idan aka yi la’akari da hauhawar farashi tun 2008.



