DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mutane huɗu sun tsira daga hatsarin jirgi a jihar Imo

-

Mutane huɗu sun tsira daga hatsarin jirgin Cessna 172 na kamfanin Skypower Express da ya yi saukar gaggawa (crash-landing) a Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe da ke Owerri, Jihar Imo, da yammacin Talata.

Hukumar Nigerian Safety Investigation Bureau (NSIB) ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 6:58 na yamma yayin da jirgin ke kokarin sauka a kan hanyar tashi da saukar jirgi (Runway 17).

Google search engine

Jirgin mai lambar rajista 5N-ASR na kan hanyarsa ne daga Kaduna zuwa Port Harcourt kafin matukan jirgin su yi gaggawar shawarar karkata zuwa Owerri.

Hukumar kiyaye afkuwar hadduran ta bayyana cewa jami’an tsaro da na agajin gaggawa na filin jirgin sun kai dauki cikin hanzari, inda aka ceto dukkan mutanen da ke cikin jirgin, ba tare da tashin wuta ba.

Rahoton ya ce biyu daga cikin matukan jirgin suna cikin koshin lafiya, yayin da sauran biyun da suka suma tun farko aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

FIFA ta sanya $60 a matsayin kudin tikitin kallon kofin duniya na 2026

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ƙaddamar da sabon rukuni na tikiti a dalar Amurka 60 ga kowane ɗayan wasannin 104 na Gasar Kofin...

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a Ingila

Ƙungiyar British Medical Association (BMA) ta tabbatar da ci gaba da gudanar da yajin aiki, bayan kashi 83 cikin ɗari na mambobinta sun amince da...

Mafi Shahara