Tauraron ƙwallon ƙafa Ahmed Musa ya sanar da yin murabus daga buga wa Najeriya ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa, bayan shekara 15 yana taka leda da Super Eagles.
Musa ya bayyana hakan ne ta cikin saƙon da ya wallafa a kafafen sada zumunta ranar Laraba, inda ya ce ya yanke shawarar ne bayan dogon tunani, yana mai nuna alfahari da wakiltar Najeriya tsawon shekaru.
Dan wasan mai shekaru 33 shi ne dan wasa mafi yawan bugawa Najeriya wasa (caps) guda 111, kuma yana daga cikin ’yan wasan zamani da suka fi samun nasara a tarihin Super Eagles.
Ahmed Musa ya kasance cikin tawagar da ta lashe Kofin Nahiyar Afirka AFCON a 2013, sannan ya kafa tarihi a Kofin Duniya inda ya zama dan Najeriya na farko da ya ci kwallaye fiye da guda a wasa daya, kana kuma ya zura kwallo a Kofin Duniya biyu (2014 da 2018).


