Jam’iyyar APC reshen jihar Plateau ta bayyana yi wa Gwamnan jihar Caleb Mutfwang maraba da shiga cikinta, bayan ficewa daga jam‘iyyar PDP.
Sakataren jam’iyyar Shitu Bamaiyi ne ya bayyana wa jaridar Punch haka, yayin tattaunawa a garin Jos.
A ranar Alhamis da ta gabata ne dai jam’iyyar APC ta bakin shugabanta na Nijeriya Farfesa Nentawe Yilwatda ta bayyana ficewar gwamnan daga PDP tare da komawa cikinta, yayin taronta a Abuja.
A cewar jam’iyyar, za ta ci gaba da bai wa gwamnan dukkanin wani goyon baya da yake bukata a tafiyarsa ta siyasa, tare da cewa kofa a bude take ga duk mai bukatar shiga tafiyar.



