Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta shiga tsakani kan rikicin shugabancin PDP, inda ta gayyaci bangarorin jam’iyyar biyu zuwa hedikwatarta da ke Abuja a ranar Juma’a.
Taron ya hada bangaren da Tanimu Turaki ke jagoranta da kuma bangaren Abdulrahman Mohammed, wanda ke samun goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban hukumar INEC Farfesa Joash Amupitan ya ce kiran bangarorin biyu ya zama wajibi ne sakamakon ta’azzarar rikicin cikin gida a jam’iyyar ta PDP.
Bayan gabatar da jawabi an shiga taron sirri, inda ake sa ran samun sasanci tsakanin bangarorin da ke rikici da juna bayan haka, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



