Rundunar sojin Nijeriya karkashin shirin ‘Operation Hadin Kai’ ta samu nasarar dakile wani hari da ‘yan ta’adda suka shirya kaddamarwa a yankin Bitta daga tsaunukan Mandara a jihar Borno.
Yayin gumurzun dai sojojin sun hallaka ‘yan ta’adda da dama kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta hannun Laftanar Kanal Sani Uba a shafinta na X, ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na daren Alhamis, inda sojojin suka gano motsin ‘yan ta’addan zuwa yankin.
Bayan fatattakar su, sanarwar ta kuma ce an samu nasarar kwato tarin makamai da sauran kayayyakin da ‘yan bindigar ke amfani da su wajen kaddamar da hare-hare kan al’umma.



