DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun halaka mutum 1,sun kuma mutane 5 a Zamfara

-

’Yan bindiga sun kai hari kauyen Fananawa da ke karamar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara, inda suka halaka mutum ɗaya tare da sace mutane biyar, a daren Asabar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ’yan bindigar sun kutsa cikin ƙauyen tun cikin dare har zuwa wayewar gari.

Google search engine

Wani mazaunin ƙauyen, Malam Sani, ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen da dare, inda suka halaka mutum ɗaya, suka sace mutane, sannan suka harbe wani mutum da ya samu mummunan rauni, wanda aka kai shi Asibitin koyarwa na Sokoto domin jinya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro suna kokari domin kubutar da wadanda aka sace kuma nan ba da jimawa ba za a ji labari mai daɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

CDD ta horas da ‘yan jarida a Katsina kan yaki da labaran karya

Cibiyar bunkasa dimokradiyya ta CDD ta horas da ‘yan jarida a jihar Katsina kan aiki mai inganci. CDD ta ce wannan na a wani yunkuri na...

‘Yan sanda sun kama wata mata a ake zargi da garkuwa da kanta

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wata matar aure mai shekaru 26 tare da wani mutum mai shekaru 30, bisa zargin yin garkuwa da...

Mafi Shahara