Ana ci gaba da samun matsin lamba daga ’yan Majalisa, jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula da a dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji da aka shirya fara aiki da su a ranar 1 ga Janairu, 2026, sakamakon zargin cewa an sauya wasu sassa bayan Majalisar Tarayya ta amince da su.
Wani dan Majalisar Wakilai, Abdussamad Dasuki (PDP, Sokoto), ya tayar da batun a zaman Majalisa ranar Laraba, inda ya ce akwai bambance-bambance tsakanin dokokin da ’yan Majalisa suka amince da su da kuma wadanda daga bisani aka wallafa a cikin jaridar gwamnati (gazette).
Sai dai Majalisar Dattawa da Ofishin Babban Lauyan Tarayya ba su yi martani ba kan zargin, lokacin da jaridar Daily Trust ta tuntube su. Dokokin harajin guda hudu sun hada da Dokar Hukumar Haraji ta Kasa, Dokar Hukumar Hadin Gwiwar Haraji, Dokar Gudanar da Haraji a Nijeriya da Dokar Haraji ta Nijeriya.
Dokokin dai an amince da su ne a Majalisar Tarayya a watan Maris, aka fitar da bayanan kuri’u a Mayu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma ya sanya hannu a watan Yuni, yayin da aka wallafa su a jaridar gwamnati a ranar 26 ga Yuni. Sai dai binciken Daily Trust ya nuna akwai manyan sabani tsakanin dokokin da aka amince da su da wadanda aka wallafa.
A wani bangare, wani dan Majalisar Wakilai, Mansur Manu Soro (Bauchi), ya ce bincikensa ya tabbatar da cewa an samu “manyan sauye-sauye masu muhimmanci” a dokokin da aka wallafa. Ya ce shi da wasu ’yan Majalisa na shirin kai batun gaban Majalisa domin neman dakatar da aiwatar da dokokin har sai an warware matsalar.



