Jam’iyyar ADC ta soki kudirin kasafin kuɗin shekarar 2026 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar, tana mai cewa kasafin tarkon bashi ne da aka lullube da sunan gyara, wanda ke dogaro da karɓar rance fiye da kima da kuma hasashen kudaden shiga da ba su da tabbas.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin, ADC ta ce kasafin kuɗin na Naira tiriliyan 58.18 bai kawo sabon abu ba illa ci-gaba da abin da ta kira sakacin tafiyar da kuɗin gwamnati, inda aka gabatar da irin kasafin shekarun 2024 da 2025 da ba a aiwatar da yawansu ba.
Jam’iyyar ta ce duk da ikirarin gwamnati na kashe Naira tiriliyan 25.68 kan ayyukan raya ƙasa, gibin kasafin da ya kai Naira tiriliyan 23.85 na nuna cewa kusan dukkan ayyukan za a yi su ne da bashi mai tsada, tana mai gargadin cewa hakan na iya jefa Nijeriya cikin ƙarin matsin tattalin arziki da ɗaure makomar ’ya’ya masu zuwa.



