DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta amince da a bayar da belin Abubakar Malami 

-

Babbar Kotu a Birnin Tarayya Abuja ta amince da belin tsohon ministan shari’ar Nijeriya Abubakar Malami, SAN, wanda ke fuskantar  zarge-zargen cin hanci daga hukumar EFCC.

Umurnin kotun ya fito ne a ranar 23 ga Disamba, 2025, inda mai shari’a Justice Bello Kawu ya yanke hukuncin amincewa da belin Malami bayan sauraron roƙon gaggawa (motion ex-parte) da lauyansa ya shigar, tare da la’akari da hujjar da aka gabatar a gaban kotu.

Google search engine

Kotun ta umurci Malami da ya miƙa fasfo dinsa na ƙasashen waje, tare da cika sharuddan beli kamar yadda EFCC ta tanada tun da farko. Daga cikin sharuddan akwai bayar da masu tsayawa masa  mutum biyu, ciki har da Darakta Janar na wata hukumar shari’a da kuma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Augie/Argungu.

Har ila yau, kotun ta amince da sake farfaɗo da sharuddan belin da aka cika a ranar 28 ga Nuwamba, 2025, tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 5 ga Janairu, 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

INEC ta yi watsi da shugabancin PDP tsagin Tanimu Turaki

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba za ta amince da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP da...

Majalisar Dattawan Nijeriya ta fara muhawara kan kasafin kudin 2026 na Nairan tiriliyan 58

Majalisar Dattawan Nijeriya ta fara muhawara kan kasafin kuɗin shekarar 2026, inda shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele daga Ekiti Ta Tsakiya, ya jagoranci tattaunawar...

Mafi Shahara