Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji, tana mai cewa rikice-rikicen da suka taso sun girgiza amincewar jama’a da tsarin dokar ƙasar.
Shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.
Kungiyar ta ce zargin sauya dokokin bayan Majalisar Tarayya ta amince da su ya tayar da manyan tambayoyi kan gaskiya, tsari da sahihancin aikin majalisa.
Wannan dai ya biyo bayan abin da jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Abdulsammad Dasuki (PDP, Sokoto), ya yi ikirarin cewa dokokin da aka zartar sun bambanta da waɗanda aka fitar a cikin kundin gwamnati. Tun daga lokacin, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da wasu ‘yan majalisa ke kira da a dakatar da dokokin.
A cewar Osigwe, dokoki masu girma irin haka dole ne su fito ta hanya mai tsabta da ɗaukar alhaki. NBA ta bukaci hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakin gaggawa domin yin cikakken bincike a fili, domin kare tsarin mulki kwanciyar hankalin tattalin arziki da kuma tabbatar da bin doka da oda, tare da dawo da cikakkiyar amincewar jama’a ga aikin majalisa.



