Tarayyar Turai, tare da ƙasashen Faransa da Jamus, sun yi kakkausar suka ga matakin Amurka na haramta biza ga wasu ’yan Turai da ke yaki da kalaman ƙiyayya da yaɗa ƙarya a kafafen intanet, suna mai cewa matakin ba shi da hujja.
Gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta saka haramcin ne a ranar Talata kan ’yan Turai biyar, ciki har da tsohon kwamishinan EU ɗan Faransa, Thierry Breton, bisa zargin takaita ’yancin faɗar albarkacin baki da kuma tsaurara dokoki kan manyan kamfanonin fasaha na Amurka.
Hukumar Tarayyar Turai ta ce tana yin Allah-wadai da matakin, tare da jaddada cewa ’yancin faɗar albarkacin baki muhimmiyar ƙima ce da Turai da Amurka ke rabawa. Ta kuma yi gargaɗin cewa za ta iya ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Rahoton Reuters ya ce lamarin na iya ƙara rarrabuwar kai tsakanin Amurka da wasu ƙasashen Turai kan batutuwan tsaro, kasuwanci, siyasa da dokokin kafafen sada zumunta, musamman bayan EU ta ci tarar dandalin X na Elon Musk kan karya wasu dokoki a intanet.



