DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu ya nuna jarumta wajen aiwatar da tsare-tsare masu wahala a 2025 – Jam’iyyar APC

-

Jam’iyyar APC ta ce Shugaba Bola Tinubu ya nuna jarumtaka ta musamman da jajircewa wajen tafiyar da Nijeriya cikin sauye-sauyen tattalin arziki da na gwamnati masu wahala amma suka zama dole a shekarar 2025.

A cikin rahoton ƙarshe na shekara kan halin ƙasa, wanda Seye Oladejo, Sakataren Yada Labarai na APC na Jihar Legas ya sanya hannu, jam’iyyar ta ce 2025 ta kasance lokacin da ake buƙatar shugabanci mai ƙarfin hali da yanke shawara mai wuya.

Google search engine

Jam’iyyar ta yi suka ga wasu ’yan siyasa da suka yi amfani da wahalhalun sauye-sauyen don nuna Nijeriya a matsayin ƙasa mai gazawa domin cin moriyar siyasa, inda ta ce wannan adawa babu kishin ƙasa sai dai manufar cutar da ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Akwai bukatar dole sai ‘yan kwallon Super Eagles sun inganta wasansu matukar suna son nasara – Eric Chelle

Kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya bayyana cewa har yanzu Nijeriya na da damar ingantawa a gasar Cin Kofin Afirka ta 2025 duk da nasarar...

Hukumar EFCC ta ki bin umurnin kotu inda ta ci-gaba da tsare Malami

Ofishin Abubakar Malami, SAN, ya yi tir da yadda EFCC ta ki bin umarnin kotun FCT Abuja na a saki Malami bayan ya cika sharuddan...

Mafi Shahara