Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su rungumi haɗin kai, juriya da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, yana mai cewa gwamnatinsa za ta cigaba da kare ’yanci da lafiyar kowa ba tare da la’akari da addini ba.
Tinubu ya bayyana haka ne a saƙon taya murnar Kirsimeti na shekarar 2025 da ya fitar a ranar Laraba, inda ya taya Kiristoci a Nijeriya da sauran sassan duniya murna, yana mai cewa Kirsimeti lokaci ne na tunani kan haihuwar Annabi Isa Almasihu da saƙon zaman lafiya, ƙauna da fata.
Tinubu ya ce saƙon Almasihu a matsayin jagoran zaman lafiya ya dace sosai a wannan lokaci da Nijeriya ke fuskantar ƙalubale iri-iri, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa na jajircewa wajen tabbatar da ’yancin addini da kare jama’a daga duk wani nau’in tashin hankali.
Haka kuma ya yaba da gudummawar da Kiristoci ke bayarwa wajen ci-gaban Nijeriya, yana mai kira da a yi amfani da lokacin Kirsimeti wajen ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin ’yan ƙasa.



