Jagoran Kwankwasiyya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce tabarbarewar tsaro a Nijeriya ba gazawar sojoji ba ce, illa dai rashin ƙwazon shugabannin siyasa.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a Kano yayin ƙaddamar da rundunar Kano State Neighbourhood Watch Corps da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa, inda aka gabatar da jami’ai 2,000 da aka horas domin taimakawa tsaron al’umma.
A cewarsa, sojojin Nijeriya jajirtattu ne kuma kwararru, amma abin da aka rasa shi ne ƙwazon siyasa, musamman daga Babban Kwamandan Rundunonin Tsaro, yana mai jaddada cewa gwamnati ta samar da kayan aiki, makamai da horo ga jami’an tsaro.
Tsohon Ministan Tsaron ya kuma yaba wa gwamnatin Kano kan kafa rundunar tsaron unguwanni, yana mai cewa mataki ne da ya dace domin fuskantar ƙalubalen tsaro, musamman a yankunan iyaka da makwabtan jihohin.



