Jam’iyyar Afirka ta Kudu ta dan gwagwarmayar adawa da Turawa Julius Malema (EFF) ta yi Allawadai da yadda Nijeriya ta amince da harin Amurka a cikin kasar kan ‘yan ta’adda.
A cikin wata sanarwa, EFF ta nuna damuwa cewa Najeriya ba ta kalubalanci matakin na Amurka ba, tana gargadin cewa irin wannan yarda na iya zama wani abu mai haɗari da ka jaddada cewa gwamnatocin Afirka ba sa iya kare kansu daga matsin lambar ƙasashen waje.
Haka kuma EFF ta dage kan cewa wannan mataki na gwamnati na iya buɗe ƙofa ga tsoma bakin ƙasashen waje a nahiyar Afirka nan gaba.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta kare kanta, tana mai cewa an amince da kaddamar da harin ne bayan tattara bayanai na sirri da kuma tsara dabarun aiki.



