Jagoran darikar Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya umarci a bai wa ‘ya’yan ‘yan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu da suka rasu damar tsayawa takara a karkashin jam’iyyar NNPP domin maye gurbin iyayensu.
Cikin wata tattaunawa da DCL Hausa ta yi da shugaban jam’iyyar NNPP na Kano Dr Hashim Sulaiman Dungurawa, ya tabbatar da cewa an cimma matsayar ne bayan da Kwankwaso ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da kuma iyalan mamatan a gidansa da ke Kano.
A cewar sa, amince musu su tsaya takarar don wakiltar kananan hukumomin Ungoggo da Municipal a zauren majalisar dokokin Kano, ya zo ne duba da irin gudunmawar da iyayensu suka bayar wajen hidimtawa al’umma.
Dungurawa ya ce suna kyautata zato tare da sa ran cewa Sa’ad Aminu Sa’ad, da kuma Nabil Aliyu Daneji za su kwatanta irin rawar da iyayensu suka taka a fagen siyasa da kuma aikin hidimtawa al’umma.



