Zakirou Zakari da Noura Hassan ne ‘yan kokawar da za su yi fafatawar karshe a yammacin wannan rana ta Lahadi 28 ga watan Disamban 2025, a gasar takobin Nijar da ke gudana a jihar Tahoua.
‘Yan kokowar da dukkanin su suka kasance ‘yan jihar ta Tahoua mai masaukin baki, sun yi nasarar kai wa wannan mataki ne bayan karawar wasan kusa da na karshe da aka yi a safiyar wannan rana, inda Zakirou Zakari ya yi nasarar kada Mati Siley na jihar Maradi yayin da shi kuwa Noura Hassan ya yi nasarar kada Chaibou Ardji na jihar Maradi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun ‘yan jiha guda sun zo matakin karshe ba, domin kuwa a baya bayan nan jihar Dosso ma ta taba kafa wannan tarihi inda Noura Hassan da Kadai Abdou da aka fi sani da Issaka Issaka suka yi karon karshe.
A yanzu dai abin jira a gani shi ne wanda zai yi nasarar lashe wannan gasar ta kokawar cin takobin na kasa karo na 46.



