Guinea ta takaita amfani da TikTok, YouTube da Facebook yayin jiran sakamakon zaben shugaban kasa.
Gwamnatin Guinea ta takaita shiga shafukan sada zumunta na TikTok, YouTube da Facebook, yayin da kasar ke jiran sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a Lahadin da ta gabata.
Kungiyar sa ido kan harkokin intanet ta NetBlocks ta bayyana cewa an samu tsaiko da katsewa wajen shiga wadannan shafuka ta manyan kamfanonin sadarwa na Orange da MTN, lamarin da ya shafi miliyoyin masu amfani da intanet a kasar.



