Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da fashewar wani abu a babban Asibitin Bagudo da ke karamar hukumar Bagudo ta jihar a Talatar nan.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta jihar SP Bashir Usman ya fitar a Birnin Kebbi, inda ya tabbatar cewa rundunar ta ƙillace wajen bayan jin ƙarar fashewar da aka da asubahin Talata, 30 ga Disamba, 2025, a harabar asibitin.
Ya ce rundunar tsaro ta hadin gwiwa wacca ta kunshi ’yan sanda, sojoji da jami’an sa-kai ta garzaya wurin cikin gaggawa dan tabbatar da tsaro.
Kazalika ya bayyana cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoton ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbanin faruwar lamarin.



