Daga 1 ga watan Janairun, 2026, bankunan Nijeriya za su fara cire harajin N50 kan duk wanda ya tura kudi da ya kai ₦10,000 ko sama da haka, bisa tanadin sabuwar dokar haraji (Tax Act) da aka kafa.
Jaridar Punch ta rawaito cewa bankunan kasuwanci irinsu UBA da Access Bank, ne suka fara sanar da kwastomominsu game da aiwatar da dokar kafin fara aiki da ita.
A cewar UBA, sabon tsarin ya canza daga yadda ake yi a baya, inda za a rika cire N50 sau ɗaya kacal kan kowane harkar tura kudi da ta kai adadin da aka kayyade.
Bankin ya ƙara da cewa wanda ya tura kuɗi ƙasa da N10,000 ba za a caje su ba, haka kuma masu albashi an keɓance su daga harajin.



