Kasashen Nijar,Burkina Faso da Mali sun sanar da kakaba takunkumin biza ga ’yan ƙasar Amurka, a matsayin martani ga dokar hana shige da fice da Gwamnatin Amurka ta kakaba wa wasu ƙasashe, mafi yawansu a nahiyar Afirka.
TRT Afrika ta rawaito cewa Burkina Faso ta bayyana cewa za ta aiwatar da irin matakin sanya takunkumin biza ga Amurka kamar yadda ta ɗora wa ’yan ƙasarta.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Burkina Faso ta jaddada cewa ƙasar na mutunta kowace ƙasa da kuma daidaito a hulɗar ƙasashe, tare da bayyana cewa tana buɗe ƙofofi ga haɗin gwiwa da dukkan abokan hulɗarta, muddin ana mutunta juna da muradun ɓangarorin biyu.
Kazalika kuma ƙasar Mali ta sanar da ɗaukar irin wannan mataki, inda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce daga yanzu za ta ɗora wa ’yan Amurka sharuddan daidai da waɗanda Amurka ke kakaba wa ’yan Mali,ita ma ƙasar Nijar ta shiga cikin jerin ƙasashen da suka nuna martani kan wannan dokar.



