Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa ta ceto mutane 1,023 da aka sace, tare da kwato bindigogi AK-47 guda 189 da alburusai 4,338, a sumame daban-daban da ta gudanar a Arewa maso Yammacin Nijeriya cikin shekarar 2025.
Babban kwamandan runduna ta 8, Sakkwato, Manjo Janar Ibikunle Ajose, ya bayyana hakan yayin bikin ba da kyaututtuka da aka gudanar a ranar Laraba a birnin Sakkwato.
Manjo Janar Ajose ya ce nasarorin sun samu ne ta hannun rundunae Operation FANSAN YAMMA, wanda ke yaki da ta’addanci da ’yan bindiga a yankin.
Ya ƙara da cewa daga cikin nasarorin akwai kwace babura 305 da ’yan bindiga ke amfani da su, dawo da dabbobi 4,123 da aka sace, da kuma hallaka wasu manyan shugabannin ’yan bindiga.



