Kasashen Benin da Niger sun kori jami’an diflomasiyyar juna a wani mataki na ramuwar gayya, bayan shafe kusan shekara biyu ana takun-saka a tsakaninsu, a cewar majiyoyin diflomasiyya.
Dangantakar kasashen ta tabarbare ne tun bayan da sojoji suka kwace mulki a Niamey a watan Yulin 2023.
Gwamnatin mulkin sojan Niger dai na zargin Benin da yunkurin tayar da hankula, zargi da Cotonou ke musantawa.
Rikicin ya kara tsananta bayan dakile yunkurin juyin mulki a Benin a farkon watan Disambar jiya. Duk da cewa Benin ba ta zargi Niger kai tsaye ba, ana ci gaba da nuna shakku kan rawar da Niamey ka iya takawa.
A ‘yan kwanakin nan, Benin ta kori wani jami’in leken asiri da dan sanda da ke aiki a ofishin jakadancin Niger a Cotonou.
Idan za a tuna, an dakile yunkurin juyin mulkin Benin na 7 ga Disamba ne da taimakon Najeriya da Faransa, yayin da aka samu yaduwar labaran karya a kafafen sada zumunta cewa an kifar da gwamnatin kasar da ke yankin Sahel.
Niger na cikin kawancen AES ta Burkina Faso da Mali, kasashen da suka fice daga ECOWAS, wadanda ke kusantar siyasa da Rasha, tare da sukar kasashen gabar teku na yammacin Afirka da ke da alaka da Faransa, ciki har da Benin da Ivory Coast.




Comment:Allah yana tare da maigaskiya ako yaushe.