Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta ɗauka na kama Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro.
Ramaphosa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, inda ya ce Afirka ta Kudu na tare da al’ummar Venezuela kan abin da ya faru.
Ramaphosa ya kuma yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya UNSC da ya ɗauki mataki cikin gaggawa domin cika aikinsa na samar da zaman lafiya da tsaro a duniya.



