Wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hare-hare kan wasu al’ummomi a jihar Katsina, inda suka sace mutane da dama.
Shaidun gani da ido sun shaida wa gidan talabijin na Channels ta wayar tarho a ranar Talata cewa harin ya faru ne a daren Litinin, bayan da ’yan bindigar suka mamaye yankunan, suka kwashe tsawon lokaci suna aikata ta’asa da firgita mazauna wuraren.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ’yan bindigar sun fara kai hari a Unguwar Alhaji Barau, daga bisani suka wuce Gidan Dan Mai-gizo da Gidan Hazo, duk a Unguwar Na’alma da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Duk da haka, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, yayin da har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka kashe ko waɗanda aka sace ba.



