Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce babu wani gwamna ko mutum guda da ke da iko da jam’iyyar APC. Ya bayyana cewa dukkan manyan matakai da ake dauka a jihohi ana tsara su ne daga matakin kasa, ba a bar su a hannun jihohi ba.
Yilwatda ya fadi hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin Sunset na gidan rediyon Jay FM a Jos, Jihar Filato. Ya ce APC jam’iyya ce da ke aiki da tsari, ba da son rai ko motsin zuciya ba, yana mai jaddada cewa gwamna, sanata, shugaban karamar hukuma ko shi kansa shugaban jam’iyya ba su da cikakken iko a kanta.
Shugaban ya kara da cewa APC ta guji kafa majalisar amintattu domin kauce wa rikici, yana mai cewa jam’iyyar mallakin al’umma ce kuma mutane su ne amintattun APC, sabanin wasu jam’iyyun da wasu tsirarun mutane ke rike da dukkanin tsarinsu.




Ruwanku ya rage, kuma batun cewar Talakawa ko kuma Al’umma ne Amintattun APC wannan maganar banza ce. Ni shawarata ga APC shi ne kowa ya tsaya matsayin sa, mu Talakawa fatanmu shi ne Allah ya kaimu 2027 lafiya, za su sha mamaki