Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Sanata Datti Baba-Ahmed, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2027. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taro da jam’iyyar ta gudanar a sakatariyarta ta kasa da ke Abuja.
Baba-Ahmed ya ce burinsa na tsayawa takara ba ya da alaka da ficewar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi, zuwa jam’iyyar ADC. Ya jaddada cewa tun kafin zaben 2023 yake da burin tsayawa takarar shugaban kasa, yana mai cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba shi dama duk da addininsa da kabilarsa.
Hakazalika ya ce zai bi doka da ka’idojin jam’iyya da na INEC kafin fara kamfen. Shugaban jam’iyyar Labour Party na kasa, Julius Abure, ya yaba masa bisa ci-gaba da kasancewa cikin jam’iyyar duk da rade-radin sauya sheka bayan ficewar Peter Obi.



