Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya, Mohammed Idris, ya nesanta kansa daga wani rubutu na siyasa mai taken “Malagi 2027”, wanda ke hasashe kan zaben gwamnan Jihar Neja na 2027. Ma’aikatar ta ce an wallafa rubutun ne ba tare da sanin ministan ko amincewarsa ba, lamarin da ya kai ga dakatar da mataimakin da ya rubuta shi.
A wata sanarwa da Mataimakin Ministan kan Harkokin Watsa Labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar a ranar Laraba, an ce ministan ya bukaci jama’a su yi watsi da rubutun gaba daya. Sanarwar ta jaddada cewa ministan na mayar da hankali ne kacokan kan aikinsa na gwamnati, ba tare da tsoma kansa cikin maganganun siyasa ba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an fara bincike kan lamarin tare da dakatar da mataimakin da ya rubuta rubutun nan take. Haka kuma, ta jaddada cewa Ministan da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, na da kyakkyawar alaka ta fahimtar juna, inda ta ce duk wata jita-jita kan siyasar 2027 na iya lalata wannan hadin kai.



