Rahotannin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe naira tiriliyan 1.98 a matsayin tallafin wutar lantarki cikin watanni 12, daga Oktoba 2024 zuwa Satumba 2025.
A cewar rahoton, an kashe Naira biliyan 471.69 a zangon karshe na 2024, Naira biliyan 536.4 a zangon farko na 2025, Naira biliyan 514.35 a zangon na biyu, sannan Naira biliyan 458.75 a zango na uku na 2025 kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
NERC ta bayyana cewa wannan tallafi na biyo bayan kasancewar kudin wutar lantarki a kasa da kudin da ake kashewa wajen samar da ita, wanda ya tilasta wa gwamnati rufe gibin ta hanyar tallafi. Rahoton ya ce ana aiwatar da tallafin ne kai tsaye ta hanyar rage kudin da kamfanonin rarraba wuta ke biya wa Hukumar Sayen Wuta ta Kasa (NBET).
Duk da karin kudin wuta ga masu amfani da Band A tun Afrilun 2024, nauyin tallafin bai ragu ba. Hakan ya sa Ministan Wuta, Adebayo Adelabu, da masana ke jaddada cewa tsarin tallafin wuta ba mai dorewa ba ne, tare da kiran a mayar da tallafin ne ga talakawa kadai.



