DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Trump ya gargadi Republican da su yi nasara a zaben tsakiyar wa’adi gudun kar a tsige shi

-

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce dole ne jam’iyyar Republican ta lashe zaɓen tsakiyar wa’adin Majalisar Dokoki a 2026, in ba haka ba, jam’iyyar Democrat na iya neman tsige shi kan shugabancin.

Trump ya yi wannan gargadin ne yayin jawabi ga ‘yan majalisar Republican a wani taro a Washington inda ya ce rashin samun rinjaye a majalisar zai iya hana manufofin gwamnati gudana kuma ya fallasa hukumarsa ga bincike, inda ya bukaci ‘yan Republican su daina rikice-rikicen ciki.

Google search engine

Shugaban na Amurka ya kuma yi kira ga jam’iyyarsa su wayar da kan masu zaɓe kan manufofin Republican da suka shafi jinsin maza da mata, kiwon lafiya da ingancin zaɓe, musamman ga masu fama da hauhawar farashin rayuwa.

Hakazalika, ya yi hasashen cewa jam’iyyar Republican za ta samu nasara mai girma a zaɓen tsakiyar wa’adi mai zuwa, duk da zargin da ake masa na wasu batutuwa da suka shafi gaskiya a Washington.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Akwai gibi mai tarin yawa da muka gano cikin sabbin dokokin harajin Tinubu a Nijeriya – Kamfanin haraji na KPMG

Kamfanin haraji na KPMG, ya bayyana cewa ya gano manyan kura-kurai, a cikin sabbin dokokin haraji na Nijeriya, duk da burin da gwamnati ke da...

Za a yi zabukan ‘yan majalisar dokoki da kananan hukumomi a Benin

Kasar Benin Republic za ta gudanar da zaɓukan ’yan majalisar dokoki da na ƙananan hukumomi a ranar Lahadi, wata guda bayan wani yunkurin juyin mulki...

Mafi Shahara