Rundunar ‘yan sanda a Nijeriya ta kawar da yunkurin kai hari da sace yara a Kasuwan Magani, Jihar Kaduna, inda suka ceto yara maza da mata guda 76 ba tare da wani rauni ba.
A cikin sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Kakakin yada labarai na ‘Yan Sanda, CSP Benjamin Hundeyin, ya ce an samu sahihin bayanan sirri a ranar 5 ga Janairu 2026 cewa wasu yan bindiga na shirin kai hari da sace yara daga motocin da ke wucewa a yankin.
A yayin aikin, an kama mutane uku da suka hada da Jonathan John mai shekaru 25; Oliver Magaji, 27; da Bitrus Sawaba, 23.
Binciken farko ya nuna cewa, an kama su ne suna shirin kai yaran wasu sassa na kasar domin aikin yara da sauran ayyukan gida. Yaran da aka ceto suna cikin koshin lafiya a hedkwatar rundunar har sai a same iyayensu ko masu kula da su.
Rundunar ta tabbatar da fara cikakken bincike don gano cikakken abin da ya faru da kuma gano duk wani mai hannu a ciki kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
‘Yan sandan sun sake jaddada kudurinsu na kare rayuka da dukiyoyi, tare da rokon jama’a su bayar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen dakile aikata laifuka.



