Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi hasashen cewa hauhawar farashin kayayyaki a kasar zai sauka kasa da kashi 10 cikin 100 a shekarar 2026, lamarin da ya ce zai taimaka wajen inganta rayuwar ‘yan kasa da kuma kara habakar tattalin arziki (GDP).
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a, 9 ga Janairu 2026, yayin da Shugaba Tinubu ke yaba wa kamfanonin Nijeriya da masu ruwa da tsaki a kasuwar zuba hannun jari bisa samun Naira tiriliyan 100.
Shugaban ya ce cimma wannan matsayi alamar tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da farfadowa ne, inda ya bukaci ‘yan kasa da ‘yan kasuwa su kara zuba jari a Nijeriya, yana mai tabbatar da cewa shekarar 2026 za ta fi alfanu ga masu zuba jari sakamakon ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatinsa.



