Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin barazanar sake kai hare-haren a Nijeriya idan aka ci gaba da kashe Kiristoci, duk da musanta wa da gwamnatin Nijeriya.
Trump, ya bayyana cewa Amurka na iya kara kai hare-haren soji a Nijeriya idan aka ci gaba da kashe Kiristoci a kasar, kamar yadda jaridar New York Times ta rawaito a wata hira da aka wallafa ranar Alhamis, 8 ga Janairu 2026.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters,ya rawaito cewa Trump ya yi wannan jawabi ne yayin da ake tambayarsa kan harin soji da Amurka ta kai Nijeriya a ranar Kirsimeti, inda sojojin Amurka suka ce sun kai harin ne kan ‘yan kungiyar IS a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya bisa bukatar gwamnatin Nijeriya.
Trump ya kara da cewa duk da cewa Musulmi ma ana kashe su a Nijeriya, a cewarsa Kiristoci ne suka fi fuskantar hare-hare, ra’ayin da gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da shi, tana mai jaddada cewa ‘yan ta’adda na kashe Musulmi da Kiristoci baki daya, ba tare da nuna wariya ta addini ba.



