Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekaru 28 bisa zargin lalata da ’yarsa ta cikinsa ’yar shekara takwas, lamarin da ya faru a ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar ranar Alhamis, an ce wanda ake zargin ya kira yarinyar zuwa bandaki, inda ake zargin ya aikata laifin a kanta ba tare da amincewarta ba.
An ce an kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda ranar 31 ga Disamba, 2025,bayan karɓar rahoton, tawagar bincike ƙarƙashin jagorancin CSP Kadiri Danjuma, DPO na Alkaleri, ta gaggauta zuwa wurin, ta kai yarinyar asibiti domin duba lafiyarta, sannan ta kama wanda ake zargin.



