Jam’iyyun siyasa a Greenland sun bayyana cewa ba sa son zama ‘yan Amurka, bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sake nuna yiwuwar amfani da karfi domin kwace yankin Greenland mai arzikin ma’adanai.
A wata sanarwa da suka fitar a daren Juma’a, shugabannin jam’iyyun biyar na majalisar Greenland sun ce makomar yankin dole ta kasance a hannun ‘yan Greenland kadai. Wannan na zuwa ne bayan Trump ya ce Amurka za ta dauki mataki kan Greenland ko suna so ko ba sa so.
Jam’iyyun sun ce, ba sa son zama Amurkawa, ba sa son zama ‘yan Denmark, sun fi son zama ‘yan Greenland, suna masu jaddada cewa su ne kadai ke da hakkin yanke shawarar makomar yankin kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Kasashen Denmark da sauran kawayen Turai sun nuna damuwa kan kalaman Trump, duk da cewa Amurka na da sansanin soja a Greenland. Trump dai ya ce mallakar yankin na da matukar muhimmanci ga tsaron Amurka, musamman ganin karuwar ayyukan sojojin Rasha da China a yankin.
Firaministan Denmark, Mette Frederiksen, ta gargadi cewa duk wani hari kan Greenland zai kawo karshen tsarin tsaron NATO. Sai dai, Trump bai dauki ikirarin Denmark da muhimmanci ba kan yankin, yana mai cewa kasancewar Danes sun taba sauka a can shekaru daruruwa da suka wuce ba yana nufin mallakar kasar ba.



