Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi dan shekara 20 bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara shida a karamar hukumar Alkaleri. Rundunar ta ce an kama Bilal Ya’u ne bayan mahaifin yarinyar ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda.
Mai magana da yawun rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Janairu, 2026, inda ake zargin matashin ya yaudari yarinyar zuwa wani gini da ba a kammala ba, sannan ya aikata mata fyade. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Gwamnati da ke Alkaleri domin duba lafiyarta da kula da ita.
‘Yan sanda sun ce matashin ya amsa laifinsa yayin bincike, tare da bayyana cewa ya taba aikata irin wannan laifi ga yarinyar tun a shekarar 2024, inda a wancan lokacin aka gargade shi kawai. Rundunar ta tabbatar da cewa bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu bayan kammala bincike.



