Tsohon gwamnan Plateau kuma jigo a jam’iyyar PDPn jihar Jonah Jang ya bukaci Gwamna Caleb Mutfwang da ya sauka daga kujerarsa a kuma sake gudanar da zabe.
Wadannan kalamai sun biyo bayan ficewar Gwamna Caleb daga jam’iyyar PDP tare da komawa APC mai mulkin Nijeriya.
Tsohon gwamnan ya fadi haka ne a wani taron jam’iyyar PDP ta jihar Plateau, inda ya ce tunda gwamnan ya fice daga jam’iyyar da ta ba shi damar samun kujerar, to kamata yayi ya sauka.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi na nuna damuwa da tsarin Nijeriya da ya bai wa ‘yan siyasa damar sauya sheka a cikin jam’iyyu, yana mai bayyana hakan a matsayin tarnaki ga tsarin dimukuradiyya.



