DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Atiku ya zargi Tinubu da tsoratar da masu faɗar ra’ayi kan gwamnatinsa

-

Madugun adawa a Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya buƙaci gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta sakin Abubakar Salim Musa (@AM_Saleeeem), wani matashi da aka tsare bisa sukar tabarbarewar tsaro a ƙasar.

Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, bayan kungiyar Amnesty International Nigeria ta sanar cewa an kama Musa ba tare da dalili ba a daren 11 ga Janairu, 2026, kuma ana tsare da shi a gidan yarin Keffi.

Google search engine

A cewar Amnesty International, lamarin na nuni da yadda ’yancin faɗar albarkacin baki ke ƙara fuskantar barazana, musamman ga matasa, inda mutane ke fuskantar barazanar kamawa da tsarewa ba bisa ka’ida ba saboda bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta.

Atiku ya ce tsare Abubakar Salim Musa abin damuwa ne da ke nuna takurawa ga masu adawa, yana mai cewa laifinsa kawai shi ne sukar tabarbarewar tsaro a Arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya, yana jaddada cewa maimakon gwamnati ta magance matsalolin tsaro da ake nunawa, ta koma tsoratar da masu sukarta—musamman a fili.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kotun kolin Nijeriya ta yi watsi da karar da ake zargin Manjo Al Mustapha da hannu wajen halaka matar Abiola

Kotun Kolin Nijeriya ta yi watsi da shari’ar da aka shigar da Manjo Hamza Al Mustapha, kan zarginsa da hannu wajen halaka Kudirat Abiola, matar...

Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea Bissau sun saka ƙarshen shekarar 2026 don gudanar da zaɓe a ƙasar

Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea-Bissau sun ce za a gudanar shugaban ƙasa a ranar 6 ga Disambar 2026, bayan da suka kifar...

Mafi Shahara