An shiga rana ta huɗu da gwamnatin ƙasar Iran ke ci gaba da katse intanet a faɗin ƙasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da ake cewa ita ce mafi girma a Iran cikin sama da shekaru uku.
Kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito, ƙungiyar sa ido kan harkokin intanet ta NetBlocks ta bayyana cewa zuwa safiyar Litinin, katsewar intanet ɗin ta kai sama da sa’o’i 84 ba tare da yankewa ba.
Rahotanni sun nuna cewa katsewar na zuwa ne a lokacin da dubban ’yan ƙasar ke ci gaba da fitowa kan tituna domin nuna adawa da manufofin gwamnati, duk da ƙoƙarin da hukumomi ke yi na takaita sadarwa da yada labarai.
Masu sa ido na kasa da kasa na bayyana damuwa cewa katse intanet na iya ƙara ta’azzara take haƙƙin bil’adama, tare da hana duniya samun cikakken bayani kan abin da ke faruwa a Iran a halin yanzu.



