Gwamnatin Jihar Sokoto ta ce mutanen da aka gani a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, ’yan garin Tidibale ne a Karamar Hukumar Isa, amma ba ’yan bindiga suka kore su ba, kamar yadda ake yadawa.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a na Fadar Gwamnati, Abubakar Bawa, ya fitar a ranar Alhamis 15 ga Janairu, 2026, inda ya ce an ɗauki matakin kwashe mutanen ne na ɗan lokaci bayan samun jita-jitar cewa ’yan bindiga na shirin kai hari yankin.
Sanarwar ta ce kansilan mazabar Tidibale, Dayyabu Sani, ne ya kai rahoton jita-jitar ga Shugaban Karamar Hukumar Isa, Alhaji Sherifu Kamarawa, wanda daga nan ya bayar da umarnin kwashe mutanen zuwa hedkwatar karamar hukumar a matsayin matakin kariya. Daga bisani, an mayar da mutanen lafiya zuwa gidajensu, yayin da jami’an tsaro suka ƙara sintiri a yankin.
Gwamnatin Jihar Sokoto ta kuma sanar da amincewa da kafa sansanin sojoji na Forward Operations Base (FOB) a Tidibale domin ƙarfafa tsaro, tare da gargadin jama’a kan yaɗa jita-jita da siyasantar da batutuwan tsaro.
Hakazalika, ta kuma bukaci ’yan ƙasa da su haɗa kai da hukumomi wajen yaki da ’yan bindiga, tare da tona asirin masu bai wa miyagu bayanai a cikin al’umma.



