Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya jagoranci manyan jami’an gwamnati wajen sakin tsuntsaye a bikin Ranar Tunawa da Sojoji ta 2026, a matsayin alamar kudirin Nijeriya na zaman lafiya, hadin kai da ’yanci.
An gudanar da bikin ne tare da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio; Babbar Alkalin Alkalan Nijeriya, Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun; Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, da sauran manyan baki. An wallafa bidiyon taron ne a ranar Alhamis ta hannun Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Nijeriya kan Harkokin Watsa Labarai (Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa), Stanley Nkwocha.
Tsuntsayen da aka saki sun tashi nan take, abin da masu kallo suka bayyana a matsayin alama ta kimar sadaukarwa da jaruman sojojin Nijeriya da suka rasu suka bayar domin kare kasa.
Ana gudanar da Ranar Tunawa da Sojoji a ranar 15 ga Janairu duk shekara, domin girmama ’yan rundunar sojin Nijeriya da suka sadaukar da rayuwarsu a bakin aiki, ciki har da Yakin Basasa, ayyukan wanzar da zaman lafiya, da kuma yaki da ’yan ta’adda da masu tayar da kayar baya.



