Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta musanta rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tuge inda suka harbe tare da jikkata mazauna yankin.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa abin da ya faru ba harin ‘yan bindiga ba ne, illa rikici da ya barke tsakanin wasu mambobin Civilian Joint Task Force (CJTF) da kuma wasu da ake zargin tsoffin ‘yan bindiga ne ‘yan asalin kauyen Tuge Mai Zuri da ke karamar hukumar Musawa a jihar Katsina.
A cewar DSP Abubakar Sadiq Aliyu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:35 na safiyar Asabar, 17 ga Janairu, 2026, lokacin da rikici ya kaure tsakanin bangarorin biyu, har aka yi musayar wuta. Hakan ya janyo jikkatar mutane hudu sakamakon harsasan da aka harba inda daya daga cikinsu ya rasu bayan an kai shi asibiti, yayin da sauran uku ke karbar magani.



