Obasanjo ya goyi bayan takarar shugabancin Nijeriya na Kwankwaso da Peter Obi a 2027 tare da cewa Atiku ba zai iya kalubantar Tinubu ba.
Wani babban jami’i a jam’iyyar ADC ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Cif Olusegun Obasanjo shi ne ya fara tunanin hadin gwiwar siyasa tsakanin Mista Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa.
A cewar jami’in jam’iyyar, Cif Olusegun Obasanjo ba kawai ya amince da sauya sheƙar Mista Peter Obi zuwa jam’iyyar ADC ba kadai, har ma ya bukace shi ya yi aiki tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin su nemi tikitin shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Tsohon Shugaba Obasanjo ya fito fili yana goyon bayan Mista Peter Obi a zaɓen 2023, inda ya yi kamfe tare da tara masa magoya baya a faɗin Nijeriya domin ƙalubalantar ɗan takarar jam’iyyar APC Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A wata budaddiyar wasiƙa da ya rubuta a ranar 1 ga Janairu, 2023, Cif Obasanjo ya bayyana cewa ko da yake babu wani ɗan takara da ya kasance tsarkakke gaba ɗaya, amma idan aka kwatanta halayya, tarihin aiki, fahimta, ilimi, da ƙwazon aiki, Peter Obi, wanda ya kira almajirinsa, ya fi sauran ‘yan takara cancanta wajen jagorantar ƙasar a halin da take ciki.



